Kamfanin sadarwar MTN ya fito da wani sabon tsarin raba data ta yadda masu amfani da layin na MTN za su iya samun kyautar 30gb na data.
Ga masu amfani da tsarin MTN Betertalk idan suna dannan waɗannan lambobi na *131*65# zasu iya siyan 1gb akan ₦200 kuma idan suka loda katin ₦200 za a basu kyautar data da kuɗin kira har ₦500 da haka zaku tara kuɗin har ku kai ₦30,000 sai ku juya su su koma data ta hanyar MTN swap.
A wani labarin kuma.
Jarumin fim ɗin A Duniya, Abdulwahab Awarwasa ya rasu
Daya daga cikin jarumai’n masana’antar fim ta Kannywood, Abdulwahab Awarwasa ya rasu.
An rawaito jarumin ya rasu a jiya Litinin, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Daya daga cikin jaruman masana’antar ne, Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Abale ne ya wallafa labarin rasuwar jarumin a shafinsa na Facebook.
Ya ce “Innalillahi Wainna Innalillahi Rajiuna, Allah Ya jikanka da rahama,
Allah Ya sa bakin wahalar ke nan. Allah Ya kula da bayanka..”
Tuni jaruman masana’antar suka shiga bayyana ta’aziyyarsu da alhinin rasuwar jarumin.
Kafin rasuwarsa ya kasance daya daga cikin ma’aikatan bayan fage, sannan kuma jarumin barkwanci.
Sannan ya kasance daya daga cikin manyan jaruman cikin fim din ‘A Duniya’ wanda suke fitowa a matsayin mugaye.
Awarwasa ya kasance ya iya fitowa tare da bayar da abin da ake so a cikin fim, ya kasance kwararren dan wasa.
Daily Nigerian Hausa ta lura cewa tuni kafafen sadarwa su ka cika da hotunan marigayin, tare da addu’o’in neman Rahma da jin kai gare shi.
Views: 134
