Ɗan sanda ya mance bindigarsa wajen karɓar cin hanci a Ghana

Wani ɗan sanda a ƙasar Ghana ya shiga tsaka-mai-wuya bayan da ya mance da bindigarsa a cikin wata motar haya.

Direban motar ya yi zargin cewa ɗan sandan ya bar bindigarsa ne bayan da ya karɓi cin hanci.

A wani bidiyo da ake yadawa a shafukan soshiyal midiya, an ga wani direba yana rike da bindiga kirar AK-47.

Direban motar hayan ya mayar wa ‘yan sanda bindigar inda ya bayyana musu cewa dan sanda ne ya mance da ita a cikin motarsa a lokacin da ya shiga domin kabar cin hanci.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *