Yesu ya bani damar saduwa da duk maccen da nayi sha’awarta a Matsayina na Fasto—Osifo

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Osifo Kyiri Osofo Kyiri Absom ya bayyana wa tsohuwar matarsa cewa yana da damar dirka wa duk yawan matan da ya ga dama ciki.

Wannan ya biyo bayan yadda aka samu zargi kan ya yi lalata da mata da dama kuma duk babu wacce bai haihu da ita ba.

Ya zargi tsohuwar matarsa da rashin mutunta shi tare da yada karairayi akan shi yayin da ake ganin darajarsa a matsayinsa na fasto.

Osofo Kyiri Absom bai bayyana cewa aurensu ya rabu ba kawai, ya kuma ba kansa damar auren duk matan da ya ga dama.

Ya yi ikirarin cewa yana da damar kara yawan mata, cikin masu zuwa cocinsa ga sauran yawan matan da ya ajiye a gida.

Kuma ya ce matarsa bata isa ta dakatar da shi daga yin abubuwan da ya ga dama ba.

Kamar ya ce:

“Idan ina so, zan iya saka wasu daga cikin ku a jerin matana. Aikin babba ne amma kuma a hankali lokaci ma kara tafiya ina kara yawan mata. Kuma ina da damar yin hakan kuma zan yi.

A matsayinsa na mutumin da ke kusa da Ubangiji ya ce zai ma iya dirka wa duk matar da ya ga dama ciki.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *