Ɗan damfara ya damfari Kuɗi a baki har naira 800k
Wannan duniyar tazo ƙarshe kuma dukkanmu muna buƙatar yin hankali sosai domin abin da idona ya gani a yau ban yi tsammanin haka ba.
A hanyata na dawowa daga bankin (UBA) kusa da Alexa plazer a Ikorodu, jihar Legas, sai na hangi wata mata ta nufo inda nake, ina kallon fuskarta sai na lura tana kuka sosai na ji tausayin yadda take kuka. Sai na matsa kusa da ita na tambayeta me ya faru?
Yace min wai yanzu wani mutum ne ya yaudare ta a banki na tambaye ta yaya? ta ce ta je banki domin ta ajiye kudi har 800k na cinikin da tayi a kasuwar ta na wata guda.
Matar taci gaba da cewa:
“Ina isa na je na cika takardar ajiya bayan na cika, sai wani mutum a kusa da ni ya roke ni da na ba shi aron biro domin ya cike nashi, bai fi minti daya ba ya mayar mini da biron, kwatsam sai na ganni tsaye a wajen bankin (alhalin kuma da farko ina ciki) ina dubawa sai naga babu kuɗina, da sauri na koma ciki na tambayi jami’an tsaro ko sun ga abin da ya faru?
Sai kawai suka ce min ai sunga na raka matashin waje na ba shi kuɗin da suke hannu na da kuma biro. Nan take na fara kururuwa ina ihun cewa juju ne ya damfare ni. Nace musu bansanshi ba bazan iya jurewa 800k ba!!!! Na ji kamar ƙarshen duniya ne.
Don Allah a kiyaye kada kowa ya ari wani alkalami a banki, domin gujewa ƴan damfara.
From Opera News
Views: 15
