Wani matashi ya rasa ransa sakamakon ɓarkewar hatsaniya a wajen yaƙin neman zaɓe

Rikicin Siyasa yayi sanadiyar rasuwar wani matashi a karamar hukumar Gwarzo Mazaɓar Kutama.

Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin mutanan kwankwasiyya da al’ummar karamar hukumar Gwarzo, a mazaɓar kutama.

Rikicin ya faru ne a yau litinin yayin yaƙin neman zaɓen NNPP a garin kutama, inda suka hau al’ummar gari da sara har takai ga rasa rai.

Sai dai ‘yan gandujiyya ɓangaren Apc na zargin ‘yan kwankwasiyya da kashe musu mutum ɗaya wanda baiji bai gani ba.

Muhd Sani Balare Ajingi

Views: 39

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *