Nayi Alƙawarin gina matatar man Fetur a yankin Kudu maso Gabas—Atiku Abubakar

Nayi Alkawarin Gina Matatar Man Fetur A Kudu Maso Gabashin Najeriya– Cewar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A Jam’iyar PDP Atiku Abubakar.

Atiku Abubakar ya ce aikin hakar mai zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin.

Ɗan takara shugaban kasa a ƙarƙashin jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin magoya bayan jam’iyyar a wani gangami da aka yi a Bauchi a ranar Talata.

Ya ce aikin hakar danyen mai a Arewa maso Gabas zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin da ma kasa baki daya.

“Gano danyen man fetur da kuma aikin hakar mai tsakanin Bauchi da Gombe wani ci gaba ne mai koshin lafiya wanda zai taimaka matuka wajen farfado da arzikin yankin Arewa maso Gabashin Najeriya,” inji shi.

Ya kara da cewa “Idan aka zabe mu a matsayin shugaban kasa gwamnatinmu za ta ci gaba da aikin bincike da hako albarkatun kasa domin amfanin yankin da ma kasa baki daya.”

Atiku Abubakar ya kuma yi alkawarin ba da kuzarinsa wajen karfafa matasa ta hanyar samar da ayyukan yi ta hanyar sana’o’in hannu da kanana da matsakaitan sana’o’i.

“Wannan zai samar da dandali ga matasa da mata marasa aikin yi don dogaro da kai,” in ji shi.

Atiku Abubakar wanda ya nuna farin cikinsa da dimbin jama’a, ya yabawa jama’a musamman magoya bayan jam’iyyar PDP da suka fito domin tarbarsa.

Ya bukaci jama’a da su marawa Gwamna Bala Mohammed baya a yunkurinsa na sake tsayawa takara domin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na alheri.

Shima da yake jawabi, Mohammed ya bada tabbacin zaben Abubakar dari bisa dari a jihar. Ya kuma bukaci al’umma da su baiwa Abubakar dukkanin goyon bayan da ake bukata domin samun nasarar zaben shugaban kasa.

Mohammmed ya bayyana shi a matsayin wanda ya fi kowa kwarewa wajen kai kasar nan zuwa kasar da aka yi alkawari.

Daga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya

By News Agency Of Nigeria.

Views: 23

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *