Kotu ta ɗaure matar da ta tilasta wa ƴan mata 4 yin karuwanci shekara 21 a gidan yarin

Kotun Anambra ta yanke wa wata mata hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari bisa samun ta da laifin tilasta wa ‘yan mata 4 masu karancin shekaru yin karuwanci.

Babbar kotun majistare da ke Awka, jihar Anambra, ta yanke ma wata mata mai suna Success James, ‘yar shekaru 35 hukuncin zaman gidan yari bisa laifukan tursasa yara, cin zarafin yara, satar yara.

Tun da farko dai an kama wandda ake tuhuma a Onitsha kuma an gurfanar da ita a gaban babban kotun majistare da ke Awka, a wani lokaci a cikin watan Disamba, 2022, saboda sace wasu ‘yan mata guda hudu tare da yin lalata da su.

Kwamishinan mata da walwalar jama’a na jihar Anambra, Hon Ify Obinabo, tare da hadin gwiwar ‘yan sanda ne suka ceto wadannan ƴammata a watan Disamba, 2022.

Wadanda suke da, shekaru tsakanin 13 zuwa 15, dukkansu ‘yan jihar Akwa Ibom, an kubutar da su ne a wani samame da aka kai a gidan karuwai a jihar Delta mallakin wandda ake tuhuma da kuma kula da su.

Mai laifin ta gurfana a gaban Kotun bisa tuhume-tuhume 8 da, lalata da yara da kuma satar yara, sannan an same da laifuffuka bakwai daga cikin tuhume-tuhumen da kotun keyi a kanta.

Da take yanke hukunci a kan karar, shugabar majistare, Genevieve Osakwe ta samu Success James da laifin aikata laifukan.

Babban Alkalin kotun, ya bayyana cewa duk hukuncin zai gudana ne a lokaci guda, ba tare da wani zabi na tara ba.

A shaidu daban-daban da suka gabatar a gaban kotun Honourable, wadanda abin ya shafa sun shaida wa kotun cewa wata aunty Success ce ta yaudare su da yin sana’ar karuwanci, inda ta shaida musu cewa ta samu damar yin aiki a Agbor da ke jihar Delta, inda za su rika sayar da kayan shaye-shaye a wata kasuwa. gidan giya; amma da isa Agbor sai suka gano cewa aikin karuwanci ne aka kawo su suyi.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, kwamishinan mata da walwalar jama’a Hon. Obinabo ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka gaggauta gudanar da shari’ar, ya kuma bayyana cewa an shigar da yaran makaranta, yayin da wadanda suka fi son koyon sana’o’i sun fara koyon sana’o’in da suka ga dama a cibiyar koyon sana’o’i ta jihar, da ke Awka.

Hon Obinabo ya ci gaba da yin gargadin cewa gwamnatin jihar Anambra ba za ta amince da duk wani laifi ba, kuma za ta ci gaba da yin iyakacin kokarinta wajen ganin yara da mata a jihar sun samu adalci, a duk lokacin da aka tauye musu hakkinsu.

By lindaikejisblog

From Opera News

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *