Masu garkuwa da mutane sun bukaci Naira Miliyan ₦150 Sako kwamishinan C’River N150m.
Bayan kwashe kwanaki takwas da yin garkuwa Kwamishinan Mata ta Jihar Kuros Riba, Farfesa Gertrude Njar, masu garkuwar sun bukaci Naira miliyan 150 domin a sako ta.
An yi garkuwa da kwamishinan ne a unguwar Mayne Avenue-Atamunu dake yankin Calabar ta kudu da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Fabrairu.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na Jihar Kuros Riba, Eric Anderson, a lokacin da yake sanar da ‘yan jarida faruwar lamarin, ya ce an tuntubi ‘yan sanda da babban sakataren ayyuka na musamman Dr Alfred Mboto.
Ya kuma nuna damuwarsa akan irin wannan mummunan ta’adda cin dake faruwa a Jihar.
Njar tare da wasu kwamishinonin gwamna Ben Ayade ne ya rantsar da su kwanan nan.
By Kazeem Tunde
From Opera News
Views: 6
