Labari da ɗumi-ɗumi Wata Budurwa Ƴar Shekara 18 ta Binne Jaririn da ta Haifa Cikin Rami Da Ranshi.

Wata Budurwa Ƴar Shekara 18 ta Binne Jaririn da ta Haifa Cikin Rami Da Ranshi.

Wata yarinya ‘yar shekara 18 daga jihar Akwa Ibom da aka fi sani da Bright ta binne sabon jaririn da ta haifa a raye nan da nan bayan ta haifi jaririn.

Rahotanni daga Premium Times sun bayyana cewa, Bright ta binne jaririn da ta haifa a cikin wani kabari mara zurfi a gidan iyayenta bayan ta haihu.

Yayin da Bright ke binne jaririnta, makwabciyarta ta fahimci abin da ke faruwa ta kukan jaririn, sai suka sami damar tono jaririn daga cikin kabari mara zurfi, sannan suka tsaftace ta, suka yi yunkurin kai jaririn zuwa asibiti, amma cikin rashin Sa’a Jaririn ya Mutu.

Lokacin da Bright ta yi hira da jaridar Premium Times, ta ce, “Ban san cewa ina da ciki ba, kwatsam na fara ganin wani jariri yana fitowa daga jikina, sai na fara kuka, lokacin da jaririn ya fito, ya riga ya mutu, don haka sai na fara kuka. Na yanke shawarar in binne shi a cikin kabari mara zurfi”.

Ta kara da cewa “Na so in ajiye ta a cikin kabari har sai in mahaifiyata ta dawo don in nuna mata jaririn,” in ji Bright. Sai dai makwabtan nata ba su yarda ba, sun ce Bright ta binne jaririnta da rai, jaririn nata bai mutu ba lokacin da ta binne shi, karya kawai take yi. Har kukan jaririn ne ya ja hankalinsu.

Kamar yadda Bright ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin tana da ciki ba har sai da ta fara ganin jaririn da ke fitowa daga gare ta, wani likita ya yi adawa da cewa ba zai yiwu mace mai ciki ta san tana da ciki ba, wasu kuma ba za su sani ba, amma dole ne mace ta sani. domin jaririn zai dinga harbawa shima yana yawo a cikinta.

Source by miracleikwor

From Opera News

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *