CBN:” ya karyata jita jitar cewa za’a rufe hanyoyin tura kudi da kiran waya a ranar zaɓe”

Babban Bankin Najeriya wato CBN ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa zata rufe hanyoyin tura kudi na bankuna wato “transfer”

Babban bankin yace bashi da kudurin kawo tsaiku na tura kudi ko karba a lokutan zabe mai zuwa na ranar Asabar.

Tun bayan jita-jitar da ake ta yaɗawa a tsakanin al’umma cewar za’a rufe sabis ɗin tura kuɗi da kiran waya a ranar zaɓen 2023.

Babban Bankin Najeriya wato CBN ya fito ya ƙaryata wannan jita-jitar, inda ya tabbatar da cewa bashi da wani buri na ƙuntatawa mutane da hanasu walwala ranar zaɓe.

source: alfijir hausa

Views: 41

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *