Za’a kafa ƙungiyar Musulmai wacce za tayi gogayya da ta kiristoci wato CAN a Najeriya

Don samar da murya daya an yi kira ga Malaman Najeriya da su kafa kungiya.

Daga Excellency Tameem Bn Alhassan Kano.

Sako zuwa ga manyan malaman Nigeria Tare da Girmamawa Allah ya kara maku lafiya da nisan kwana ya Albarkaci Rayuwarku.

Sheikh Dahiru usman Bauchi.
sheikh Abdullahi balalau.
Sheikh sani yahaya Jingir.
Dr sani umar Rijiyar lemu.
Dr Bashir Aliyu umar.
Sheikh Aminu ibrahim Daurawa.
Dr. Ahmad Mahmud Gumi.
Prof.Ahmad ibrahim maqari.
Sheikh Ibrahim zazzaki.
Sheikh muhammad Bn uthman.

Muna fatan dan Allah su samar mana da wata kungiya Babba me magana da yawu daya kan Abinda Ya Shafi Harkan Musulunci a fadin Nigeria baki daya, kamar dai yanda kungiyar kiristoci suka samar da tasu tun a baya Mai Taken “CHIRISTAN ASSOCIATION OF NIGERIA (CAN), muna fatan idan sun samar mana da wannan kungiya duk wani shugaba da yake neman shugabanci a wannan kasa lalle a zauna dashi domin fada masa Abin da zai yi mana a kasa kuma lalle ya saka Hannu kuma dole a mana Abin da muke bukata.

Bangaran mabiya kuwa matukar an aiwatar da wannan kungiya me magana da yawu daya tabbas za muyi biyayya kuma duk wanda malaman nan suka ce mu zaba shi zamu zaba ,matukar aka aiwatar da wannan Al’amari wallahil Azim babu wani shugaba daya isa ya keta Alfarmar musulmai ,babban Abin da ke haifar mana da matsala akwai Rashin hadin kai amma matular zamu hada kanmu babu makawa sai munga canji a Rayuwar mu.

Views: 29

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *