Yanzu Yanzu: Miji ya kama matan shi biyu suna Maɗigo a gidan shi

LAHAULA WALA QUWATA ILLAH BILLAH HATTARA DAI MATA!!!

Wani Mutum ne magidanci mai matan aure guda biyu Salihai ne masu nagarta Uwar gida da amarya yana jin dadin zama da matansa

Wadan nan Matan suna yin Whatsapp a wani Group din Mata sai su ka hadu da wata mata Shugaban ‘Yan Madigo ta jihar ita matar ‘Yar asalin jihar Kaduna ce amma tana aure a kano a Unguwar Nasarawa

Wannan Matar Shugabar ‘Yar Lesbian din sai ta dinga bibiyar Matan nan har tana ziyartarsu daga karshe ta yi sanadin jefa su cikin wannan fasikancin na Lesbian har matan mutumin su ka dinga neman junansu

Ma’ana dai Uwar gida da amarya su ka dinga Madigo a tsakaninsu a gidan mijinsu Wa’iyyazu bilah su ka yi nisa a harkar abisa ziga da koyarwar wannan Shedaniyar matar Shugaban kungiyar ‘Yan Madigo

Ranar da dubunsu zata cika Mijin da kansa ya kama Matan nasa Uwar gida da amarya suna tafka wannan masha’ar fasikancin Madigo a gidansa a dakin amaryarsa Saboda tsananin firgita da ya yi Mutumin sai da ya fadi aka kai shi asbiti

Bayan Mijin ya farfado ya dawo gida nan ya shiga bincike akan ya aka yi haka ta faru daga karshe dai ya gano duk da yadda aka yi Salihan Matansa su ka shiga wannan mummunar Dabi’ar

Yanzu haka Mijin ya yi alwashin sai ya dauki matakin doka akan matar da ta shigar da iyalansa wannan fasikancin ita wannan Shugabar ‘Yan Madigon ba jahila bace tana da ilimin addini da na zamani amma ba karamar annoba bace tana shigar da mata da yawa wannan harkar kuma har tutiya take yi da cewa ita ‘Yar Lesbian ce in zaka kira sunanta tafi son ka kirata da ‘yar Madigo

kuma abin takaici mijinta ya san duk abin da take aikatawa amma shi Sam abin bai dame shi ba babu ruwansa

Anan Ina kira ga Mata Ku dinga Lura da mutanen da zaku dinga haduwa da su a Media ko a rayuwa ta zahiri duk Wanda Ku ka ga tafiyarku ba daya bace Ku raba hanya da su wannan ita ce mafita

Allah ya kyauta ya shirya ya yi mana tsari da afkawa zuwa ga halaka ya tsare mana imanin mu.

Views: 171

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *