ABIN A YABA: Wani Matashi Ya Zabi A Samar Da Ruwan Sha A Kauyensu Maimakon A Ba Shi Naira Milyan Shida Domin Ya Gina Kansa
Ko kun taba cin karo da labarin matashin da ya yi irin wannan sadaukarwa irin ta Umar Dan Fulani matashi da ya gwammace a kai ruwa kauyen su akan ya samu kyautar miliyan shida ya gina kansa.
GA YANDA ABIN YA FARU – :
Wani matashi ya sanya mutanen sa cikin farin ciki bayan ya hakura da kyautar naira miliyan 6 daga wani kamfanin da ya yi musu aiki. Maimakon tayin tallafin miliyan shida da aka yi masa ya nemi a samar da ruwa a kauyen su mai suna Sabon Garin Kawagga, gunduman Tulai a karamar hukumar Toro jihar Bauchi.
Matashi wanda aka fi sani da Umar Danfulani ya samu aiki da wani kamfanin Turawa a online mai suna SHIBNOBI, matashin ya yi aiki ne da kamfanin, inda ya yi ta kokarin tallata kamfanin a Nijeriya a kafar sadarwa.
Ganin kokarin da na yi wajen tallata shibnobi a Nigeria, sai wata rana Baban jami’in gudanarwa kamfanin tasu shibnobi mai suna CLIFF FETTNER ya kira shi yace masa Umar mene sana’arka, a Nijeriya kai ma mu tallafe ka kamar yadda ka tallafa mana?
Sai Umar ya ce masa shi dalibi ne amma sana’ar da ya keyi shine wankin motaci kuma da ita ya dauki nauyi karatun sa tun sakandire har zuwa jami’a a matsayin sa na maraya.
Nan take sai Manajan ya masa albishir cewa an yanke shawarar kamfanin zai ba shi kyautar kudi har naira milyan 6 a masayin tallafi, shi ma ya je ya karfafa aikin sa domin ya dogara da kan sa a rayuwa.
Umar yace ina jin wannan albishir din sai zuciya ta ta ce min lallai Miliyan 6 a wajena kudi ne masu yawa wanda zan iya azurta kaina, in taimaki dangi na a matsayina na maraya.
Amma ni ina ga lokaci yayi da ni ma zan sadaukar don magance masalar ruwan sha wa kauyen mu wanda muke fama da ita kimanin shekaru 20,
Kuma kullum da mu ake neman wanda zai kawo mana dauki. Tunda na yi aiki Online kuma Allah ya taimaka na samu har miiliyan 6 ta hanyar basira ta to wajibi ne ni ma na sadaukar domin na taimaki al’umma ta.
Umar ya ce bayan na yanke wannan shawara Sai na Kira Manajan nace masa in zai yiyu ina son maimako abani kudinnan ,ina son su yi anfani dashi wajen samarwa kauyena ruwan Sha,!!
Wanda shine matsalar da ta addabi al’umma na kuma ni daya ne cikin mutane da muka shafe tsawon shekaru muna cikin wahalar ruwan Sha !!
Wannan Tunani nawa ya baiwa kamfanin makaki Sai da suka yi zama na musamman Suka Girmama wannan shawari nawa kuma kai tsaye suka amince kuma suka umurcenni da in kawo kasafin kudin da za a kashe wajen samar da ruwan.
Cikin yardan Allah na nemi kanfani mai suna BARADEZ NIGERIAN LIMITED, yakawo musu kasafin million takwas( 8)da za a kashe domin samarwa da ishashen ruwan sha a kauyen mu,
Nan take suka Amince suka kara Miliyan biyu cike da yarda da murna sai suka cika sauran kudin, Aka samar mana da ruwan Alhamdu Lillahi Wallahi yanzu Burina yacika mun samu ruwan sha
A kauyen mu kuma ta Dalilina Nagode ma Allah da yayi amfani Dani ya faranta Ran yan kauyen mu inji Umar!!
SARKIN GARIN KWAGGA SHIMA CIKE DA MURNA YA SHEDA MANA-:
Da muka tuntubi sarkin kwagga Malam idris kwagga yace babu abinda zamu cewa yaron nan sai dai Sanya masa Albarka da addu’an Allah ya Albarkaci rayuwan sa yanda ya faranta ran mu Shima Allah ya faranta masa nasa fiye da haka.
Sarkin yace A Addinin Muslunci ko Dabba ka shayar Allah zai Shayar da Kai Balle kuma mutane masu yawa haka mungode mungode….!
Sarkin ya Kara da cewa wani abin mamaki da Yaron nan mahaifinsa ya rasu, amma da yasamu wannan daman maimakon ya azurta kansa ko ya taimaki yan uwasa sai ya taimkemu gabaki daya, mutanen kauya wanda burin matasa yanzu su samu kudi su manta da kauyensu,
Sarkin ya Kara da cewa ina kira ga Gwannati jihar Bauchi da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafi wanna Yaron ,su bashi aikin yi tunda yagama karatunsa domin samun irin su yana da wahala, kuma wanna abun da yayi yanuna mana idan yasamu mukami zai taimaki mutane, domin ba abun duniya ne agabansa ba.
mun kyautata masa zato kuma shine wakilin mu ko Ina muna masa fatan Alheri irin wannan Yaron kadan ne cikin mutane inji Sarkin.
Views: 24
