An Kashe Wani Mutum dan ya siya naman saniya a Indiya
‘Yan sandan Indiya a ranar Asabar din da ta gabata sun bayyana cewa sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wani musulmi da aka kai wa hari saboda zargin ya siya naman sa.
Marigayin, Naseem Qureshi, mai shekaru 56, ya rasu ne a farkon makon nan, bayan da wasu ’yan daba suka kai masa hari bisa zargin yana ɗauke da naman sa, wanda kananan hukumomi suka hana sayar da shi da kuma cin sa a wasu sassan kasar.
An tattaro cewa wanda aka kashen an yi zargin sama da mutane 20 ne suka kewaye shi kuma suka kai hari, kamar yadda wata sanarwa da ‘yan sanda suka fitar a kotun, kamar yadda jaridar Al’rabiya ta ruwaito.
A cewar sanarwar da aka fitar, ‘yan sanda sun shiga tsakani, amma Qureshi ya mutu a hanyar zuwa asibiti
Views: 12
