An Kori Wasu Hatsabiban Mata Uku Masu Gadi A Gidan Yari Dake ingila, Bisa Laifin Bibiyar Maza Fursunoni Suna Masu Fyaɗe.”
Sudai waɗannan hatsabiban mata sun kasance suna aikin gadi ne a wani gidan gyaran hali dake ƙasar Ingila.
Waɗannan mata sun daɗe suna aikata irin wannan laifi, sai dai a wannan karon dubin su ta cika a dai-dai lokacin da suke ƙoƙarin faɗawa wani fursuna.
Cikin rashin Sa’a basu samu dama ba sakamakon akwai wasu jami’an tsaro da suka ankara da shigar matan bangaren fursunonin maza.
Nan take sai jami’an tsaron suka bi bayansu domin tabbatar da abinda suke zargi.
Inda a ƙarshe waɗannan jami’an suka yi nasarar kama waɗannan mata dumu-dumu , yanzu haka dai za’a gurfanar dasu a kotu domin yanke masu hukunci.
Views: 14
