Abubuwan da aka tattauna a ganawar Tinubu da zaɓaɓɓun ƴan majalisar tarayya

Shugaban Najeriya mai jiran gado, Bola Ahmad Tinubu ya yi wata ganawa da zaɓaɓɓun ƴan majalisar tarayya a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ganarwar ta zo ne ƙasa da mako ɗaya kafin zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jiha da za a yi ranar 18 ga watan Maris da muke ciki.

Ɗaya daga cikin mahalarta taron kuma zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya bayyana wa BBC abin da taron ya ƙunsa.

Ya ce an kira taron domin taya juna murna da kuma yin waiwaye game da irin matsalolin da aka fuskanta a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya da ya gabata domin tunkarar zaɓen da ke tafe.

A cewar Ndume, shugaban asar mai jiran gado ya buƙaci a ƙyale zaɓaɓɓun ƴan majalisar tarayyar su zaɓi shugabancin majalisar ta 10 ba tare da wani katsalandan ba.

Ndume ya kuma ce taron ba shi da nasaba da batun waɗanda za a tsayar a matsayin shugabannin majalisar dokoki ta 10.

Sanatan ya kuma musanta zargin da ake cewa yana neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta gaba inda ya ce “shugabanci ɗora wa mutum a ke, shugabancin majalisa, muna jira muga abin da Allah zai yi amma babban abu shi ne a yi adalci, inda ba adalci ni bana ciki.”

A nata ɓangaren, Honorable Fatima Talba ƴar majalisa mai jiran gado daga jihar Yobe wadda ta yi nasara a zaɓen da ya gabata, ta ce ganawar na da alaƙa da batun haɗin kai sai dai ta ce yanzu hankali ya karkata ne ga zaɓen da ke tafe.

“An dai yadda mu gama wannan zaɓe da za a yi a gaba, sannan a zo a yi tunani wa ya kamata ya zama a ina.” in ji ta.

source: arewa24news

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *