Najeriya na daga cikin ƙasahe 10 da ƴan ƙasar basa iya neman rancen kuɗi su samu
Najeriya, Laberiya, Ghana da Zimbabwe da wasu kasashen Afrika shida ne kasashen da suka fi kowacce kasa kudin ruwa mafi yawa a nahiyar.
Mai bincike ya bayyana cewa, yawan kudin ruwa na rage yawan kashe kudin jama’a, hakan nan yana rage samun dama ga ‘yan kasa su karbi rance.
Hakazalika, masanin ya ce, yawan kudin ruwan na hana kasa damar fitar kayayyakinta zuwa wasu kasashe, kuma hakan na karya darajar kudi.
Afrika – A cewar babban bankin Najeriya (CBN), kaso 17.5% ne kudin ruwa ga rance a Najeriya, dalili kuwa, hauhawar farashin kayayyaki ya lakume kudaden da aka ajiye, wanda ya kai akalla 22% a Najeriya a yanzu.
Illar yawan kudin ruwa ga kasa na da yawa, amma mafi munin hakan shine, yana lakume kudaden shiga tare da sanya kunci ga ‘yan kasa, musamman wajen neman rance, kamar yadda APA Hausa ta tattaro.
Yawan kudin ruwa na sanya ‘yan kasa su rasa damar cin bashin banki, wanda ke rage yawaitar siyan kayayyaki, daga karshe hakan kuma ya rage siyayya daga gama-garin mutane, kankat kuma ya shafi tattalin arzikin kasa.
Najeriya na cikin kasashen da rancen kudi ke ba da wahala
Kudaden Najeriya, sabbi da aka sauya |
Yawan kudin ruwa na kassara kasuwanci
Hakazalika, yawan kudin ruwa na iya kassara kasuwanci a kasa tare da koran masu zuwa hannun jari, wanda hakan zai shafi kasar baki daya, sannan ya karya darajar kudi.
A bangare guda, fitar da kayan haja zuwa kasashen waje ka iya zama matsala, domin dole zai rage yadda jama’a ke fitar da kayayyaki waje duk dai ta sanadiyyar yawan kudin ruwa.
Amma duk da haka, yawan kudin ruwa na sanya yawan ajiye kudi a banki tare da rage kashe-kashen kudi a tsakanin jama’a saboda mutane za su rike kudade don kuwa tsadar kayayyaki zai karu, wanda ka iya rage yaduwar kudade.
Zimbabwe ta fi yawan kudin ruwa a kasashen Afrika
Zimbabwe: 150%
Ghana: 28%
Sudan: 27.3%
Sierra Leone: 18.25%
Malawi: 18%
Angola: 18%
Nigeria: 17.5%
Mozambique: 17.25%
Egypt: 16.25%
Liberia: 15%
Source: legit hausa.ng
Views: 19
