WATÁ SABÚWA: Nagá Anáta Ihuń Mata Suna Cikó Ai Mazá Ma Na Cikó Da Cucumber, Cèwar Jamilá Ibrahim (Málamar Aji)
Idań yarinya ta bar nónuwá kamań buhu dúk a sake acé bata da kamún jiki, ta ɗan samó bra (rigar nónó) mai kyau ta zuba kayanta ta ɗaúre ance tayi ciko, wai só kuke ta sakesu warsheshe suyi ta yawo ne?

Wasu kuma túmbi garesu idań sun saka gówn sai ya fitó kaman masu juna biyu dón Allah idan sun samí abun páckaging ba za su yi ba?
Wasu Kuma duwáwunsu ne kaman an kife faranti babu tsoka idan sun saka kaya baya kyau shi yasa suke ɗan cikó dan kómai ya fito cif-cif, kunga laifinsu? Nikam bańga laifinsu ba.
Idan kaga yarinya kana so, ka so ta don Allah dan kaima kila sai an maka ciko da maganin basir ba ka da abubuwa masu inganci a jikinka kaga kuwa dole kowa yayi haƙuri da abunda ya Gani.
Ku bar mata su cike inda suke ganin yana da matsala a jikinsu dan su sami confidence, tunda ba surgery sukayi ba, da surgery ne nan ne zancé an shíga wani sabga na sabon Ubangiji.
Mazama na cikó da cucumber akace… Cèwar Jamila
Views: 74
