Rarara zai saki wakar da ya karbi N1,000 domin yi wa Buhari

Hoto Daga Rarara Multimedia

Shahararren mawakin siyasar nan a Najeriya, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara zai sake sabuwar wakar sa wacce ya rangadawa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari domin goge laifin da yan kasar ke ganin ya yi musu.

masoya Buharin dai na ci gaba da tambayar ina aka kwana a batun kudin da suka tura domin yiwa masoyinsu waka.

Wakar dai za ta zo da sabon salo domin ba irin wacce mawakin ya saba yi ce a shekarun baya ba ana sa ran sakin sabuwar wakar nan ba da jimawa ba kamar yadda wata majiya daga mawakin ta bayyanawa sashin hausa na APA.

Idan ba ku manta ba a karshen watan oktoban bara ne mawakin yan bayya cewa ba zai sake yiwa shugaban kasar Muhammadu Buhari waka ba sai idan masoyan shugaban sun biya shi kudn wakar inda ya nemi masoya Buharin da su tura masa naira 1,000 kafin ya yiwa shugaban waka.

Kunji fa menen ra’ayoyinku?

Views: 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *