Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon shiri wanda ya fi na Survival Funds

A ranar talatar da ta gabata ne Shugaban NaMuhammadu Buhari, ya kaddamar da wani sabin kwamitin rage talauci a kokarin Shugaba Buhari na ganin ya sallami talauci daga Nijeriya, yanzu haka ya kafa Kwamitin rage raɗaɗin datara da talauci a ƙarƙashin jagorancin mataimakinsa Yemi Osinbajo tare da taimakon wasu mukarrabai.

Shugaba Buhari yace “Ina cike da farin cewa wannan shiri da mu ka shata na kakkaɓe talauci da ƙuncin rayuwa ga mutum miliyan 100 an tsara shi ne ta hanyar magance kurakuran da aka ɗibga a baya, sai kuma kafa tubalin shirin daƙile fatara a fadin kasar.

Shugaba Buhari ya ce shirin Rage Raɗaɗin Talauci zai kuma binciko dalilan da ke haddasa talauci, sabubba da rabe-raben talauci ta yadda za a san irin kulkin da za ta sa domin ta yi masa kwaf-ɗaya in ji shi.

Mambobi Kwamitin sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, gwamnonin Ekiti, Sokoto, Nasarawa, Bsrno, Ebonyi da sauransu.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Karamin Ministan Kuɗaɗe, Ministar Agaji da Jinƙai, Ministan Gona da na Cinikayya.

Talakan Nijeriya dai yanzu yana fama da tsadar rayuwa na fitan hankali. Sai dai kuma a karshen makon nan da ya wuce Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya tabbatar da cewa Tattalin Arzikin Cikin Gida na Najeriya ya fara farfadowa da kyar.

Dk kuwa da cewa mafiya yawancin talakawa basu gane irin wannan lissafin na batun.
farfadowan tattalin arziki kasar ba.

Don kuwa har yanzu rashin aikin yi da ƙuncin rayuwa sun riƙe wa talakawa da marasa galihu maƙogaro, ta yadda miliyoyin ‘yan Najeriya ke iya iya samun abincin da zai ci a yini.

Yanzu haka dai masana tattalin arzikin na cewa Najeriya tana ci gaba da samun ƙaruwar haɓɓakan tattalin arzikin cikin Sabila da shirye shiryen gwamnati Buhari na Tallafawa yan kasar da suke fama da radadin talauci.

Menene ra’ayoyinku?

Views: 34

3 thoughts on “Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon shiri wanda ya fi na Survival Funds

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *