LABARI DA DUMI DUMI: Kotun kolin Najeriya ta haramtawa gwamnoni tsige ciyamomi a kasar

Hoto Daga The Nation

Babbar kotun kolin Najeriya ta na wani shiri na haramtawa gwamnonin a fadin kasar sauke wa tare da nada shugabannin kananan hukumomi 774 na fadin kasar, wata majiya ta ambato babban alkalin alkalan kasar na cewa.

“Wannan hukunci zai taikama wajen bawa shugabannin kanan hukumomin kasar yancin cin gashin kansu domin su kubuta daga hannun gwamnonin kasar da suka shafe shekara da shekaru suna yi musu mulkin mallaka”.

Idan ba’a manta ba a shekarun da suka gabata ne gwamnonin kasar suka karbe ikon gudanarwa daga shugabannin kananan hukumomin kasar inda suka shafe shekaru suna yi musu mulkin mallaka ta yadda suke cirewa tare da dasa shugaban karamar hukuma, tare da karbe ikon gudanar da kudadensu.

Kunji menene ra’ayoyinku?

Views: 35

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *