LABARI DA DUMI DUMI: Buhari zai tafi London don duba lafiyarsa

Rahotanni daga Abuja fadar gwamnatin tarayyar Najeriya na cewa,

Shugaban kasae Muhammadu Buhari zai tafi London a gobe Juma’a domin a duba lafiyarsa fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce shugaban zai tafi Landan gobe Juma’a don duba lafiyar ta sa.

A wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan cikin wata gajeruwar sanarwa da ya fitar yau Alhamis da yammaci.

Ya kara da cewa ya ce ana sa ran shugaban zai koma gida Najeriya a mako na biyu na watan nan mai kamawa idan Allah ya kaimu.

Muna fatan Allah ya ba shi lafiya yasa aje lafiya a dawo lafiya ameen.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *