Da Mijina yayin min Kishiya Gwamma ya rinƙa Kwanciya da ƴaƴan mu
Tsokacinmu na yau wani babban al’amari ne wanda shafin ya ci karo da shi, wani labari ne me ta da hankalin mai hankali, wanda yake cike da ban mamaki da al’ajabi, wanda aka nemi a sakaya suna.
Labarin dai shi ne: Wata mata ce bahaushiya, musulma, me tsananin kishin tsiya, wadda kishin nata ya wuce misali, kishi ne tamkar irin na masu tabin kwakwalwa.
Wadda ke da kusanci da matar da har ila yau ita ce ta aiko mana da wannan sakon ta ce; ‘Matar ta yi ikirari a kan cewa; Da Mijinta ya yi mata kishiya gara ya dinga amfani da yaranta mata da Allah ya ba su guda biyar, matar ta ce; a duk ranar da yake da bukata ya gaya mata wacce ya ke bukata za ta kawo masa ita da kanta’.
Wa’iyazubillah.. Ko ya za a kira hakan da shi? Wadanne hanyoyi ya kamata mata su bi domin tursasa zukatansu, da bawa kwakwalwarsu damar yin tunani me kyau ko dan gudun fadawa tarkon da-na-sani?.
Wannan ya sa mika kawo maku wannan labarin domin muji daga bakin ku.
Source: Jaridar Taskira
Views: 47
