BaKu latsa nan don kallon Bidiyon
Ba bude Boda aka yi ba, Gwamnati ta ‘kara tabbatar da matsayar ta cewa Bodojin Nigeria suna nan a rufe, abinda ake cewa shine wadanda suke shigo da kayayyakin can da ada aka hana shigo dasu an bayar da dama wa CBN ta taimaka musu da Canjin Dala daga Naira idan zasu shigo da wadancan kayayyaki ta kan iyakokin da aka saba wato ta kan ruwa.
~ Sai dai duk wanda ya fahimci wannan lamarin yasan cewa wannan da muguwar rawa gara ‘kin tashi ne, domin hakan bai zo ba sai a lokacin da Dalar ta haura Naira 1030.
Lamarin zai iya shafan Noman da Miliyoyin mutane suka yi idan har manyan Attajirai suka yi amfani da damar Canjin Kudin suka Sayo kayan suka ajiye daga nan zuwa watanni 8 masu zuwa da Daminar zata sake dawowa, barazanar da ake tunanin zata zo ne shekara me zuwa ba yanzu ba (Allah ya tsare mu ba fatan mu kenan ba).
Na uku, a yadda muka san kasar mu, wannan damar kamar wata ‘kofa aka budewa wasu suyi arziki daga kwance ba tare da sun motsa da ilimin su ko jikin su ba. Domin takardu kawai za’a yi ta cikewa cewa Kamfanina zai shigo da Shinkafa ta Naira Miliyan 500, Misali.
~ Sai a bani Canjin Kudin daga CBN sai ni kuma inje in siyar da ita a bayan fage in kwashi ribar da nake so cikin Awa daya ko biyu, sai inbi kan mutanen da nake ganin zasu sa Ido akan lallai sai na Sayo Shinkafa da Canjin da aka bani daga CBN din ko sauran hukumomi in sallame su da na Goro, suyi shiru.
Kenan a nan su waye za suyi hasara? wadanda da gaske suke shigo da kayayyakin can 43, domin zasu ga cewa ga ‘kofa an bude musu, idan sunzo shiga kuma wasu sun toshe ta.
~ Abu na hudu, tallafin da Gwamnatin zata bayar ga kasuwar Foreign Exchange shima dalili ne da nake fahimtar anyi ne domin wasu, duk da cewa za’a dan amfana wajen samun karyewar Dalar idan ba’a daina boye Dala fiye da kima ba, in kuma aka yi hoarding din ta, toh Allah ya mana Rahama kawai.
Lastly, Hausawa suka ce in za’a sha Giya Asha ta dubu (Astagfirullah), babban abinda mutane suke cewa shine in dai ba don manya aka yi ba toh a bada amfani da International Transfer using ATM Cards ya dawo, karba da tura Kudade kamar yadda ake yi ada. Duk da cewa Gwamnatin tana kare matsayar ta da cewa saboda security da dakile ta’addanci ne yasa ta dauki matakin, toh amma mu a Arewa wane ta’addanci ne ya dakata bayan an hana?
~ In dai da gaske ne sai ‘yan Crypto ma suce a dauke Takunkumin da aka kakabawa Bankuna aka hana su hada hada da Dalar kasuwar Crypto ranar 17 February 2021, domin Dalar P2P ta Black market wuta kenan🔥.
Ayi hakuri ba sukan matsayar Gwamnatin nake yi ba, tun ita na zaba, amma siyasa tayi yawa a cikin sabon tsarin ne gaskiya.
~ Na tabbata babu wadanda zasu ji zafin wannan sabon matakin kamar asalin wadanda suke shigo da kayayyakin nan na gaskiya, domin wasu zasu boye Dalar, wasu zasu mayar da ita Black market suci riba idan sun karbo daga CBN, sannan ba’a duba makomar Manoman da yanzu suke fito da kayan su daga Gona ba.
Wanda ya rubuta
Abdul-Hadee Isah Ibraheem.
Views: 92
