Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan
Wata sabuwar Malamar ta sake zuhuri, amma ni abunda ke bani mamaki, su wadannan Malaman waazin da ya fi musu dadi shine labarin aure da jima’i, tamkar dik ayoyin Qurani akan jimai aka sauko da su. Tayaya za’a yi kana zaune kana kalllon kyakkaywar mace tana bayanin jima’i wani abu bai zo maka a zuciya ba?
Bayyanar Malamai mata abune mai kyau, amma baiwa wadannan matan damar hawa mimbari suna wa’azi ana sakawa a social media da sunan addinin Musulumci ban san ina aka samo shi ba. Kuma wallahi hakan ba daidai ba ne, domin bidah ce karara da aka kawo cikin addini, mace ta tashi daga wani gari ta hau jirgi ko mota don ta je wani gari wa’azi yaushe aka yi hakan, waye yace ayi ina hujja?
Ni dai gaskiya wadannan mata ma su batsa ba su da banbancin da Muneera Abdulsalam a waje na.
©Sharif Almuhajir
Views: 68
