Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Al’mansoor Gusau, ya rabawa marubuta kyautar sabbin wayoyi kirar Android guda 40, na kimamin miliyan hudu da kuma tsabar kudi ta Naira miliyan daya
Daga Comr Abba Sani Pantami
A yau Asabar muka gudanar da Workshop na wuni guda, ga marubutan jam’iyyar APC na kananan hukumomi 6 na yankin Zamfara ta yamma, kan yadda ake amfani da kafofin sada zumunta da kuma muhimmancin shi.
Bayan an kammala taron dan uwa Al-mansoor Gusau, ya bawa marubuta 40 kyautar sabbin wayoyi kirar Android na kimamin Naira miliyan hudu, don kyauta musu, tare da bada kyautar tsabar kudi Naira miliyan, ga marubutan da mahalarta taron.
A yayin gudanar da taron, na gabatar da makala da ta shafi muhimmancin kafofin sada zumunta da irin rubutun da ya kamata matasa su dinga gudanarwa, tare da karfafa musu guiwa kan rubuce-rubuce masu amfani a kafofin sada zumunta.
Al’mansoor Gusau, ya gabatar da jawabai masu muhimmanci da suka shafi rubutu a kafofin sada zumunta, haka zalika suma sauran manyan baki sun gudanar da nasu jawabai masu muhimmanci.
An gudanar da Workshop din ne, a farfajiyar Sakateriyar Sanatan Zamfara ta yamma, da ke karamar hukumar Talata Mafara, jihar Zamfara.
Al-Mansoor Gusau, shine babban daraktan yada labarai na mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara Sanata Abdul’aziz Yari. Ba yau Al-Mansoor ya saba tallafawa marubutan Zamfara ba, ya dade yana tallafa musu ta bangarori da dama.
Bayan gudanar da Workshop na yankin Zamfara ta yamma, nan bada dadewa za’a gudanar da irin shi a yankin Zamfara ta tsakiya da yankin Zamfara ta Arewa.
Views: 23
