VIDEO: “Jerin abubuwa 5 da sumbatar masoyi ke ƙarawa macce ciki harda tsawon rai”

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Sumbatar Masoyi Na Ƙara Tsawon Rai Da Sheƙin Fuska Musamman Ga Mace, Inji Binciken Ƙwararru

Sumba hanya ce da masoya ke amfani da shi wajen nuna soyayyar su ga waɗanda suke so.

Ba ya ga masoya iyaye ma kan yi amfani da wannan hanya domin nuna soyayyar su ga ‘ya’yan su.

Wata marubuciya kuma masaniyar abincin dake inganta garkuwar jiki dake ƙasar Amurka Jeena Schreck ta bayyana wasu hanyoyin da Sumba ke inganta lafiyar mutane.

Ga Hanyoyin

  1. Sumbata Na Ƙara Danƙon Soyayya a Tsakanin Masoya:

Sumbata musamman tsakanin masoya na cikin hanyoyin dake taimaka wa mata wajen amincewa da namiji wajen yin jima’i ko aure.

  1. Faranta Rai:

Sumbata hanya ce dake faranta wa mutum rai yana kuma taimakawa wajen rage gajiya a jiki.

An ce gamsuwar da ake samu a lokacin da ake sumbatar masoyi kusan dai-dai yake da irin daɗin da wanda ke maskewa da Heroin.

  1. Inganta Fatar Mutum:

Musamman ga mata sumbatar masoyi na ƙara haske da annuri a fuskar mace ta riƙa sheƙi.

  1. Sumbata na taimaka wa mutane da dama wajen samun gamsuwa kafin jima’i. Sannan yana taimakawa wajen inganta sha’awar yin jima’i ga masoyi da masoyiya.
  2. Sumbata Na Ƙara Tsawon Rayuwa:

Wani sakamakon bincike da Arthur Szabo ya gudanar ya nuna cewa sumba na ƙara tsawon rayuwar mutane a duniya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa muddin namiji na sumbar matarsa da safe kafin ya tafi wurin aiki yana ƙara tsawon rayuwarsa domin zai tafi aiki cikin jin daɗi da anashuwa.

Views: 42

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *