Al’umar jihar Katsina sun amince su biya harajin N2,000 ga duk wani baligi—Gov Masari

Gov Masari Na Jihar Katsina

A wata sanarwa da aka fitar a safiyar yau gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, ta ce al’umar jihar ce ta amince cewa daga yanzu duk wani baligi ya rika ba da N2,000 a kowace shekara a matsayin haraji ga gwamnati domin samar da ci gaba.

Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren arzikin jihar, Alhaji Faruk Lawal Jobe ne ya shaida wa jaridar DCL Hausa hakan a Katsina.

Me za ku ce kan wannan dabarar, kuma ko kuna shirye da ku yarda da hakan a jihohinku domin ci gabanku?

Views: 6

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *