An bayyana ranar da za’a ci gaba da haska film ɗin A Duniya

Jaruman Film Ɗin A Duniya

A Duniya, wani sabon shirin Film din wasan Hausa ne da kamfani Tijjani Asase ke ɗaukar nauyin shiryawa tare da gabatarwa, wanda ake haskawa a ko wace ranar Laraba, a shafin YouTube na Zinariya Hausa TV.

Shirin wanda yake da dogon zango yau kusan makonni 4 kenan ba tare da an haska shi ba kuma babu wani ƙarin bayani da mai shirya shirin wato Tijjani Asase wanda ake yiwa laƙabi da suna Kanabaro yayi.

Sai dai a makon da ya gabata sashin Hausa na APA ya yi ƙoƙarin jin ta bakin mashiryin shirin wato Tijjani Asase don jin ta bakinsa ko ina aka kwana game da cigaba da haska film ɗin, ganin cewa shurun da aka yi ya jefa miliyoyin masoya shirin cikin zullumi.

Yayin da wasu ma ke yaɗa raɗe raɗin cewa gwamnati ce ta dakatar da haska Film ɗin, sai dai bayan mun tun tubu ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a film ɗin, ya fada mana cewa ana kan ɗaukar Season 5 ne na Film ɗin kuma za’a ci gaba da haska shi kamar dai yadda aka saba.

Ya ƙara da cewa ana sa ran cigaba da haska film ɗin zuwa ƙarshen watannan da muke ciki, ko kuma zuwa farkon watan Nuwamba mai kamawa.

Views: 50

One thought on “An bayyana ranar da za’a ci gaba da haska film ɗin A Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *