An gano wani mutumin Banu Isra’ila wanda ke zama ɗaya daga cikin mutanen da Fir’aunan Annabi Musa AS ya azabtar.
Anyi ƙiyasin cewa ya shefe fiye da shekaru 5500 a ƙarƙashin ƙasa.

A wani labarin kuma.
Mun yi cikakken shiri ko da zaɓe zai kai zagaye na biyu — Shugaban INEC
Shigabann Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya hukumar ce ta shirya tsaf ko da zaben shugaban kasa zai kai zagaye na biyu.
Farfesa Yakubu ya bayyana hakan yayin da ya ke gabatar da jawabinsa a Cibiyar “Chatham House” da ke London a kasar Birtaniya, kan irin shirin da hukumar ta yi don gudanar da zaben 2023.
Chatham House, cibiya ce da ke bincike kan al’amuran da suka shafi manufofin kasashen duniya a fannin siyasa, tattalin arziki, ilimi da shugabanci da sauransu.
“Duk zabukan da muka shirya guda uku a baya, mun shirya tsaf don gudanar da zaben shugaban kasa a zagaye na biyu – ko da hakan za ta faru. In hakan ta faru, ba mu da matsala.” Farfesa Mahmood ya ce.
Farfesa Mahmood ya kara da cewa, sauyin da aka yi wa dokokin zabe a Najeriya, ya kara taimakawa wajen gudanar da zaben a zagayen na biyu cikin sauki.
“An kara tsawaita wa’adin gudanar da zaben na zagaye na biyu, daga mako daya zuwa makonni uku, amma kuma da ma, a ko da yaushe, mu kan zauna cikin shiri ko da hakan za ta faru.” Shugaban hukumar ta INEC ya ce, a lokacin da yake amsa tambayoyi bayan gabatar da jawabinsa.
Shugaban hukumar ya kuma kore batun da wasu ke yadawa cewa za a yi amfani da ma’aikatan kananan hukumomi a maimakon farfesoshi na jami’a a matsayin malaman zabe a jihohi.
“Ba za mu iya amfani da ma’aikatan kananan hukumomi ba, ai ba zaben kananan hukumomi mu ke yi ba, akwai tsari da muke bi, kuma wannan tsari bai sauya ba.” In ji Mahmood.
Views: 22
