An kama matar da tayi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgin sama a sararin samaniya inda tace Jesus ne ya ce ta buɗe

Hoto daga New-York Post

Wata mata ƴar asalin ƙasar Benin dake zaune a ƙasar Amurka ta yi yunƙurin buɗe ƙofar jirgin sama a daidai lokacin da su ke tsaka da tafiya a sararin samaniya, inda ban take jami’an tsaron cikin jirgin suka cafke ta.

Bayan sun kama matar mai suna Elom Agbegninou wacce ta taso daga jihar Ohio zuwa Texas, daka ƙasar ta Amurka ta bayyana cewa Ubangijin ta Jesus ne ya nemu da tayi hakan.

Jami’an tsaron dai sun taru a kan matar mai shekaru 35 a yayi da take yunƙurin buɗe ƙofar gaggawa da ake kira emergency exit door a turance kamar yadda jaridar New-York Post ta ruwaito.

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *