Wani shafi sada zumunta na facebook mai suna Taƙiyya izala ya wallafa hoton ministan harkokin sadarwa a Najeriya kuma shahararren malamin addinin Islama Dr Isa Ali Fantami inda ya yi zargin cewa wai malamin ya sanya wata kwalliya a rigar jikinsa mai ɗauke da alamun Cross, sai dai idan mai karatu ya lura da kyau zai ga ba Cross neba Biro ne malamin ya soka a aljihunsa sai kuma kwalliyar aljihu ta gitta shi yasa ya nuna kamar Cross
Ga hoton Screenshot ɗin nan daga ƙasa.

A wani labarin kuma.
Yadda Shari’ar Sheikh Zakzaky da ya shigar tsakaninsa da NIA kan riƙe masa Fasfo ta kaya.
Sheikh El-Zakzaky da NIA: An Sake Ɗage Zaman Kotun Zuwa Wata Febrairu.
Bayan tsawon lokaci da aka zauna, a jiya Laraba ma kotun ta sake zama, inda mai shari’ar ya dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Fabarairu shekerar nan.
Lauyan Sheikh Ibraheem Zakzaky da Matarsa Malama Zeenah, Barrister Abubakar Marshall ya bayyana cewar zasu sake dawowa domin cigaba da zaman kuma suna jin ƙamshin nasara akan abunda suka sa a gaba.
Sai dai a bangare guda kuma Almajiran Malamin ne Mazansu da matan su suka yi dafifi a ƙofar kotun domin neman a saki Fasfo din Malamin nasu.
Idan har Mai karatu bai mantaba, tun bayan Shaƙar iskan ƴanci da jagoran mabiya Shi’a yayi tare da Matarsa Malama Zeenatudden daga tsarewar da gwamnan Tarayya tayi masu, Shehin yake son fita ƙasar waje Domin cigaba da duba lafiyarsa tare dana Matarsa Amma lamarin ya cutura.
Inda ake zargin cewa Hukumar DSS tare da haɗin kan wasu ƙungiyoyin gwamanti suka riƙe Fasfo ɗin Shehin don hanasa ko motsawa daga nan gida Nijeriya zuwa wata ƙasar Neman Lafiya.
📸 Sahara Reppters Hausa.
Views: 38
