Sannan Manzon Allah SWA ya hana mu cin abinci da hannun hagu domin rigakafin kamuwa da cuta, domin hannun hagu shi ake sawa a kazanta, don haka duk abin da mutum zai ci ya tabbata ya ci da hannun dama. Sannan ya koya mana nisantar kamuwa da annobar ciwo, cewa idan mutum yana da dama ya lashi zuma sau uku a jere da sassafe kafin mutum ya ci komai, idan aka ce sabon wata ya kama tun daga farkon watan Musulunci kafin ya kai 15 ake son ka yi, kwana uku a jere, sannan ka lasa wa yaranka suma sau uku kwana uku a jere.
In Allah ya so ka yi musu haka, to annobar da za ta zo a wannan shekara Allah za tsare su. Sannan yana daga cikin koyarwar da Malamai suka yi mana na rigakafi, mutum ya rubuta Fatiha kafa bakwai da kursiyyu bakwai da lakad ja’akum kafa bakwai, Falaki bakwai Nasi bakwai, a rubuta da tawada mai kyau a allo mai kyau a wanke da ruwa mai kyau.
Ruwan da za a wanke in an samu Zamzam an fi son haka, in ba’a samu ba an fi son ruwan Sama, in ba’a samu ba a sa ruwan rijiya. In babu kuma to sai a nemi kowa ne ruwa, sai a wanke a sha shi ma ya wadatar, domin shi Allah niyya yake kallo.
Sannan ana rubuta Ayatusshifa’a din nan guda shida da suke cikin Alkur’ani su ma a rubuta duk wata a sha a gida, wannan ma ana fatan samun kariya daga annoba, wannan fa ba wai an ce idan cuta ta kama ka za ka warke ba ne, a’a rigakafi za ka yi yadda cutar ma ba za ta kama ka ba.
Sannan Manzon Allah SAW ya hana mutum ya yi kaki ya tofar a Masallaci, Malamai likitocin Musulunci suka ce ai saboda Masallaci wurin taruwar jama’a ne, idan ka yi tana iya yiwuwa kana da wata cuta da ta kama ka a huhunka idan ka tofar, iska za ta iya dauka ta sanya wa mutane.
Sannan Manzon Allah ya ce, ku ji tsoron la’ana guda biyu, kamar yadda ya zo a ruwayar Muslim, ya ce la’ana ta farko ita ce, mutum ya yi ba-haya a kan hanyar da mutane suke wucewa, ko a inuwar bishiya. Hikimar hanawar ita ce, iska za ta iya daukar cutar da ke cikin wannan najasa taka ta kai wa mutane.
Bincike ya nuna cutar kwalara bayan garin da ake yi ne iska take daukar sa ta kawo cikin mutane sai a shaka, ko ta zuba acikin ruwa sai a yi abinci da shi ko a sha, sai a yi ta amai ana gudawa. Kamar a kauyuka yadda za ka ga ana haduwa ana wanka a wuri daya, kuma ruwan nan wani fa ba ya gudu, a ciki za a yi fitsari ko a wanke bayan gari. Manzon Allah SAW ya hana mu fitsari a cikin ruwa, sai kare lafiyarmu, to suna da yawa a yanzu dai mun fadi kusan guda ishirin da biyu a iya dan bayanin nan da muka yi.
Allah ta’alah ya yi wa abin da muka ji albarka, wassalamu alaikum wrahmatullahi Ta’alah wabarkatuhu
Source: leadership.hausa.ng
Views: 14
