Ba za’a gudanar da taron Sallar Idi a Najeriya ba

Rahotanni na cewa kwamitin Yaki da cutar Corona na Fadar Shugaban Kasa karkashin jagoranci Babbar Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ta bada shawaran dakatar da duk wani nau’in bukukuwan Sallah a jihohi shida na Nigeria, Jihohin sune KADUNA, LAGOS, OYO, RIVERS, KANO, PLATEAU da ABUJA.
Sannan kwamitin ya bada shawarwarin guda uku kamar haka.

  • A gabatar da Sallah idi a Masallatan Juma’a na Unguwanni a maimakon Filayen Idi.
  • Dakatar da Hawan Sallah.
  • Takaita ko dakatar da duk wani Taro da za’a aiwatar a cikin dakunan taro.

Dama dai tuni wasu masarautun kasar suka soke bukukuwan hawan Sallah a masarautunsu.

Views: 30

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *