Bidiyon Matashi Mara Hannu Mai Rubuta Da Ƙafa Ya Ɗauki Hankulan mutane
Masu amfani da soshiyal midiya sun yabawa wani matashi mara hannuwa bisa wata baiwa ta musamman da ya nuna duk da nakasar da yake da ita
Matashin mai suna Psammy, ya ba masu amfani da yanar gizo mamaki lokacin da ya koma yana amfani da ƙafafun sa wajen yin WhatsApp
Wasu daga ciki sun yi mamakin yadda yake yin rubutun cikin sauri, wasu kuma sun yaba masa inda suke cewa sun yi ƙoƙarin jarabawa amma sun ji ba za su iya ba
Wani bidiyon wani matashi mara hannuwa yana latsa wayar sa da yin WhatsApp ba tare da wani ya taimaka masa ba, ya ɗauki hankula sosai.
A cikin wani bidiyo da aka sanya a TikTok, matashin mai suna Psammy, ya jingina bayan sa jikin bango sannna yayi amfani da wayar sa wacce ya riƙe da ƙafar dama.
Da ƴan yatsun ƙafarsa ya shiga cikin WhatsApp kamar yana amfani da hannuwan sa.
Yayi amfani da wayar cikin sauri ta yadda wanda baya da masaniya kan naƙasun da yake da shi zai ɗauka cewa wannan rubutun da Larabci aka yi shi.
Mutane da dama sun yaba masa kan yadda yake yiwa rayuwa kyakyawar fahimta.
A wani labarin na daban kuma, wani matashi mai gundulmin hannuwa ya zama tela, ya ɗinka kaya cikin ƙwarewa a wani bidiyo.
Matashin dai ya zaɓi da ya tashi ya nemi na kan sa duk kuwa da nakasar da yake fama da ita. Hakan ya sanya ya samu yabo sosai a yanar gizo.
Source: Legit.ng
Views: 15
