Dalilin da ya sa aka daina haska film din A Duniya—Kanabaro

Ma’aboda kallon shirye shiryen fina finan Huasa na masana’antar Kannywood musamman masu dogo da kuma gajeren zango wato series, wadanda ake dorawa a shafukan YouTube, na ci gaba da jiran dakon cigaban shahararren shirinnan mai cike da harkalla mai suna A Duniya.

Wanda ake haskawa a ranar ko wace laraba a tashar Zinariya Hausa TV dake a shafin YouTube, wanda shahararren jaruminnan Tijjani Asase, ke jagoranta.

Film din dai ya bar miliyoyin jama’a masu sha’awar kallonsa a cikin gida da wajen Najeriya, cikin wani hali na dakon cigabansa, ganin cewa sama da makonni ukku kenan ba tare da an saki Film din ba sannan babu wata sanarwa.

Ko kuma karin bayani daga bangaren masu alhakin haska film din dalilin da yasa aka daina haska shi, da kuma ranar da za a ci gaba da haska shi.

Wasu dai na zargin cewa gwamnati ce ta dakatar da haska Film din yayi da wasu ke ganin sam ba haka neba, sai dai daga nan sashin Hausa na APA mun yi kokarin samun mamallakin shirin wato Tijjani Asase amma hakarmu bata cimma ruwa ba.

Amma mun samu daya daga cikin masu ruwa da tsaki game da lamarin inda ya ce za a ci gaba da haska film din amma a halin yanzu ana sake tace film din don fitar da bangarorin da bai kamata a haska kowa ya gani ba.

Views: 45

One thought on “Dalilin da ya sa aka daina haska film din A Duniya—Kanabaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *