
Tun ajiya jama’a ke tambaya me yasa ba aga Babba uba Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero a wajen Daurin aure ba.
Daga Usman A Usman
Amsa itace: Sarki Uba ne a kasa gaba daya, bisa Alada Sarki baya zuwa daurin aure ko yaje gaisuwar mutuwa saboda shi uba ne ga kowa, idan akayi mutuwa shi ake zuwa ayiwa gaisuwa haka daurin aure ba zai ware daurin auren diyarsa ita kadai yaje ba Alhalin sauran Al’umma ma duk yayansa ne.
Alhaji Aminu Dantata shine Uban zuriyar Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, shine waliyin Amarya. Hatta Mahaifin Amarya Mai Martaba Sarkin Bichi shima saboda wannan Alada yana cikin gida aka daura auren sai dai aje a tayasu murna bayan an kammala biki. Haka duk wani Sarki Mai daraja tin daga Kan Mai Alfarma Sarkin musulmi zuwa kasa sukayi illa Qalilan, Duk suna Kano Amma Basu halarci Taron daurin aure ba zai gobe in za ayi Coronation.
A gobe idan Allah ya kaimu za a gudanar da taron bada Sanda ga Mai Martaba Sarkin Bichi, Shine taron Sarakuna, wannan ne taron da Mai Martaba Sarkin Kano da sauran Sarakuna masu Alfarma zasu halarta.
Alada ce, masu neman Sani ku sani, Wanda Kuma suke neman fitina Kuma sai kuyi tayi. Idan Ana harkar Arziki ba a ta tsiya.
Views: 30
