Tasaha talabijin ta NBC ta wallafa wani faifan bidiyon da aka bayyana cewar wani daɗaɗɗen gunki ne aka tono a ƙarƙashin ƙasa a ƙasar Egypt wanda ya shafe dubban shekaru kuma ake kyautata zaton yana ɗaya daga cikin gumakan da mahaifin Annabi Ibrahim wato Azara ya riƙa ɗorawa Annabi Ibrahim ɗin tallarsu a zamanin Manzon cinsa.

A wani labarin kuma
Al’ummar Dala sun yi gangamin hana daba da shaye-shaye da sata a Kano
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Dala a jihar Kano, sun yi wani gangami na hana dabanci, shaye-shaye da sace-sace a unguwannin yankin da kewaye.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Dala ma ɗaya da ga cikin Kananan Hukumomin Kano da ke da mafi yawan jama’a.
Sai dai kuma unguwannin Ƙaramar Hukumar, wacce a cikin kwaryar birnin Kano, na fama da ayyukan ɓatagari, musamman a ɓangaren kwacen waya, haura gidaje, satar babur, faɗan raba da sauran su.
Hakan ne ya sanya su ka yi gangami, manya da yaran su a jiya Litinin domin nuna kin jinin ayyukan ɓatagari da kuma ɗaukar gaɓaran kawo zaman lafiya a yankin.
A yayin gangamin, al’ummar ya kin sun riƙa daga kwalaye da takardu da aka rubuta “say no to drugs”, “no to violence” da sauransu, inda su ka riƙa rera taken “Zaman lafiya dole!!!” “Babu ƴan daba dole”.
Daha Yusuf, Mai Unguwar Dala, ya ce an hada gangamin ne domin samar da zaman lafiya a yankin.
A cewar sa, ayyukan ɓatagari ya ishi mazauna ƙaramar hukumar, inda ya ƙara da cewa shi ne su ka ga cewa bai kamata su nade hannu su zuba ido ana abinda bai dace ba.
Ya kuma yi kira ga sauran unguwanni da su kwaikwayi al’ummar Dala don kawar da ɓatagari a cikin su.
Views: 38
