Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan
An yi jana’izar matar aure mai shekaru 42, Ammi Adamu Mamman, wacce ake zargin mijinta, Abubakar Musa mai shekaru 43 ya kashe a jihar Yobe.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce lamarin ya faru ne a Sabuwar Bra-Bra Estate da misalin karfe 4:48 na safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, 2024.
A cewar Abdulkarim, marigayiyar tana gado daya da mijin nata ne a lokacin da aka caka mata wani abu mai kaifi a wuyanta, wanda ya haifar da zubar jini mai tsanani wanda ya yi sanadiyar mutuwarta.
An yi jana’izar Ammi tare da wata mata a ranar Talata 9 ga watan Janairu a fadar Sarkin Pataskum dake Potiskum.
A halin da ake ciki, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya sha alwashin cewa duk wanda ke da hannu a mutuwar Ammi, zai fuskanci fushin doka
Views: 1919
