HOTUNA: “Wani Pastor kenan lokacin da yake tashi sama zuwa Aljanna kamar yadda yace”

/aLlLwl-n3XA?si=PjLJuMb-VrYq5Y5o

Abin ban al’ajabi wani fasto ya bayyana cewa yana zuwa Aljanna ya dawo kamar yadda yaci.

/AYI2Kq_mNWM?si=sd5m1vX6FJunTmfB

Wani pastor kenan yayin da yake tashi sama zuwa aljanna (kamar yanda ya fada).

Za ku iya ganin mambobin cocin nasa suna masa bankwana.

A wani labarin kuma.

Ƴan bindiga sun kashe mutane 70 a Abuja babban birnin Najeriya.

Masu garkuwa da mutane sun kashe mutane 70 a Abuja babban birnin Najeriya a shekarar 2022 kadai.

A cewar bayanai da aka samu daga wata jami’ar leken asiri ta ‘yan asalin kasar, Beacon Consulting, ta bayyana cewa an samu ta’addancin tsaro guda 194 a dukkan kananan hukumomin FCT guda shida.

Kimanin mutane 70 ne ‘yan bindiga da wasu masu laifi suka kashe tare da sace 194 a babban birnin tarayya Abuja a shekarar 2022.

A cewar bayanai da aka samu daga wata jami’ar leken asiri ta ‘yan asalin kasar, Beacon Consulting, ta bayyana cewa an samu ta’addancin tsaro guda 194 a dukkan kananan hukumomin FCT guda shida.

A ranar 6 ga Disamba, 2022, an yi garkuwa da mutane bakwai da suka hada da wani tsohon dan sanda da Fasto daya, yayin da wasu maza biyu suka mutu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a unguwar Kubwa da ke babban birnin tarayya Abuja.

A ranar 12 ga watan Oktoba, wasu ‘yan bindiga sun sace wani mazauni a Maitama tare da kashe mutum daya. Kwanaki shida kafin harin, ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka kashe wani ma’aikacin gwamnatin tarayya, sannan suka gudu da gawarsa.

A watan Yunin wannan shekarar ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wani makiyayi a unguwar Kwali da ke Abuja. A ranar 20 ga Afrilu, ‘yan bindiga sun sace ‘yan uwa hudu a yankin Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja.

A watan Fabrairun 2022, an yi garkuwa da wani basarake na Abuja a Kuje, biyo bayan sace wata yarinya ‘yar shekara 12 a unguwar a ranar 1 ga Fabrairu.

Da yake mayar da martani ga rahotannin a wata hira da jaridar PUNCH, babban sakataren yada labarai na hukumar babban birnin tarayya, Anthony Ogunleye, ya ce an samu saukin tsaro a babban birnin tarayya Abuja a ‘yan kwanakin nan.

Ogunleye ya kuma yi alkawarin inganta tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi a sabuwar shekara.

Views: 36

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *