Shahararren ɗan wasan ƙwallon Duniya Cristiano Ronaldo ya sha ruwa mafi daraja a Duniyar musulmi wato ruwan Zam-Zam a ƙasa mai tsarki.

Zuwa ga Gomnoni, Malamai, Sarakuna da Alkalan Arewa
Daga Sherrif Almuhajir
Ya kamata ku lura da yawaitar talauci da matsalar ci-maka a cikin Al’ummar mu, ku hana daure ma su laifin da ya shafi Muamalat a gidajen yari. Saboda hakan yana kara ta’azzarar da masifar talauci musamman ma da ke wasu da ake daurewan suna da iyalan da suke ciyarwa.
Maimakon dauri, ina gani kamata yayi a bude babbar gona da za’a rika kai ma su laifi suna noma ta kyauta a matsayin fansar kan su daga laifin da suka aikata. Idan na bashi ne su biya shi da labor haka ma idan na tara ne.
Hakan ina ganin zai fi kyautuwa da a kama zaratan majiya karfi, kuma a daure su ana basu abinci daga hakkin yan kasa da basu yi laifin komai ba. Kuma hakan zai iya zama sana’ar wasu daga cikin su ko bayan sun gama zaman kwadagon na su, sannan ya ma fi dacewa da sabon sunan kurkukun da aka chanza zuwa gidan Gyaran Hali.
Wannan raayi ne na Almajiri Ko ya kuke gani?
Views: 28
