Ina neman mijin aure na gari koda talaka ne ina so—Zainab Abdul

Kamar dai yadda kuka sani ƴan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.

Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.

Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga ƴan mata da samari na yin abubuwan da zasu ɗauki hankulan abokansu na sada zumunta.

Wata budurwa mai suna Zainab Abdull ta bayyana cewa “Gaskiya ina son mutum na gari ya aureni ban damu idan kai talakane ba” kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter ga hoton Screenshot ɗin rubutunta nan daga ƙasa.

A wani labarin kuma.

Jam’iyyar PDP tayi watsi da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe da Shekarau yayi

Shugabancin jam’iyyar PDP na jihar Kano, tsagin Shehu Wada Sagagi, yayi watsi da taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman da aka gudanar karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau, da kuma Dakta Yunusa Adamu Dangwani, domin basu da hurumin yin hakan, kuma doka zata iya aiki a kansu.

Mashawarci a bangaren Shari’a (Legal Adviser) na PDP tsagin Sagagi, Isa Wangida ne bayyana haka, inda yace yin haka karya ƙa’idar Kotu ne, domin akwai sune da damar cigaba da riƙe jam’iyyar ba kwamitin riƙon ƙwarya ba.

Wangida ya ƙara da cewa, abinda ɗaya bangaren sukayi sun ƙarya umarnin babbar kotun tarayya karkashin mai Shari’a Jostis A.M Liman, wacce ta bayyana Muhammad Abacha a matsayin halattaccen dan takarar kujerar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP.

A ranar 5 ga wata ne dai Sanata Shekarau suka jagorancin taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP na jihar Kano, inda aka zaɓi Dakta Dangwani, Ibrahim Al-ameen Little, Mustapha Umar Mai Mansileta da sauransu.

Views: 32

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *