Jami’an tsaro sun kama matar da ta yi yunƙurin buɗe ƙofar jirgin sama lokacin da yake gudu

Jami’an tsaron jirgin sama sun cafke matar da tayi yunkurin buɗe jirgin a yayin da yake tsaka da sharara gudu a sararin samaniya.

Matar ta bayyana cewa Yesu Almasihu ne ya ce da buɗe jirgin ta faɗo zai tare ta kamar yadda tace, jirgin wanda ya taso daga New-York zuwa jihar Arizona ya sauka lafiya a halin yanzu kamar dai yacce rahotanni suka tabbatar

A fagen siyasa kuma da yake yanzu lokacin siyasar ne ganin cewa ƴan makonni ya rage a fara shirye shiryen gudanar da wannan zaɓe na 2023.

Ɗan takarar neman kujerar gwamnan jihar Jigawa a ƙarƙashin jam’iyar NNPP mai kayan mar mari ya bayyana cewa.

Ni ba barawo bane kuma nafi kowanne dan takara chanchanta da zama gwamnan jihar jigawa -Aminu Ibrahim Ringim

A yau ne a garin gumel yayin gangamin bada tutar takara ga yan takarkarrun jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, Jagora kuma mai yiwa jam’iyyar takarar gwamna a jihar jigawa wato mallam Aminu Ibrahim yace yace “Ni ba barawo bane kuma nafi kowa wanne dan takara chanchanta” saboda na shafe shekaru a gwamnati amma ban saci kudin talakawa ba, kuma duk cikinsu masu karyar bamu da kudi ba wanda ya siyar da gonar ubansa ya samu kudin, kudin kune in sun baku ku karba.

Mallam Aminu Ringim ya kara da cewa, isha Allahu idan aka zabe ni na zama gwamna cikin kwana dari zan share wannan bakin talaucin daya addabi wannan jiha, zan ingata rayuwar jama’a, ma’aikata da kuma masu rike da masarautun gargaji ta hanyar basu dama ba tare dayi musu kutse cikin sha’anin mulkinsu ba.

Daga karshe ya nemi jama’ar wannan jiha dasu zabe shi tare da Engr. Rabi’u Kwankwaso saboda talaka bashi da gata sai Allah sai kwankwaso kuma sune zasu inganta rayuwar jama’a tare da bawa matasa aikin yi.

Aminu Sani Ringim
Member, Student’s Affairs Comm.
Jigawa State NNPP Gubernatorial Campaign Organization.

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *