Jerin Birane 5 masu ɗauke da Mutane da suke rayuwa a ƙarƙashin ƙasa

Jerin Birane 5 masu ɗauke da Mutane da suke rayuwa a ƙarƙashin ƙasa

Ba rade-radi bane, tabbas akwai wasu birane dake karkashin kasa a duniya. Wasu daga cikin biranen nan sun kasance karni aru-aru kuma har a halin yanzu ana al’amuran rayuwa a cikinsu.

Birane 5 dake karkashin kasa, wurin da suke da labaransu masu cike da al’ajabi

1 Derinkuyu, Cappadocia, Turkiyya

Birnin Capppadocia na nan a kasar Turkiyya kuma yana da birane kusan 36 dake karkashin kasa, Momondo ta ruwaito.

An gano birnin ne a 1963 kuma an bude shi jama’a na shiga a 1965. An gano cewa birnin Derinkuyu ne yafi kowanne zurfi a cikin biranen.

An gano cewa ya samarwa jama’a 20,000 matsuguni a cikin shekarun da suka gabata. Yana da cibiyoyi daban-daban.

2 Shanghai Tunnels, Portland, Amurka

Yana nan a Portland, a Amurka akwai wani birni da ake kira da ramin Shanghai. Birnin dake kasan kasa na Shanghai ana rade-radin wuri ne da ya kasance dabdalar masu garkuwa da mutane.

A halin yanzu wuri ne da ya zama na yawon bude ido. Yana da otal, mashaya da sauransu.

3 Naours, Faransa

Birnin Naours na nan a arewacin kasar Faransa kuma yana da kusan dakuna 300, History.com ta ruwaito.

Yana nan a karkashin kasa kusan nisan kafa 100 kuma an fara samar dashi ne a karni na uku a matsayin wurin hakar duwatsu na Romaniya domin mazauna kauyen na amfani dashi wurin buya yayin yaki.

Akwai gidajen biredi, wurin adana dawaki, rijiyoyi da sauran abubuwa da ake samu a birnin mai cike da abun mamaki.

4 Wieliczka Salt Mine, Poland

Wieliczka wurin hakar gishiri ne dake Poland kuma wani birni ne dake karkashin kasa mai cike da abubuwan mamaki. Birnin dake da shekaru 1200 ya kasance yana samar da gishiri har zuwa 2007.

Ma’aikata a wancan lokacin suna amfani da gishirin da ake haka a wurin domin hada gumaka.

5 Birnin kasa na Beijing, China

Birnin yana nan a China kuma gwamnatin kasar China ce ta gina shi tun a 1960 saboda yaki, kamar yadda History.com ta ruwaito.

https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-lalace-zina-a-fili/

Yana kunshe da ramuka tare da dakuna. Akwai dakin kallo dake da mazaunin mutum 1000 kuma an bude shi domin masu yawon bude ido da shakatawa tun wurin 2000.

Views: 37

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *