Jerin Manyan Jihohi 10 da suka fi Yawan ƙwararrun Likitoci a Najeriya.

Jerin Manyan Jihohi 10 da suka fi ƙwararrun Likitoci a Najeriya Kwanan baya, kafofin yada labarai sun ruwaito ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige yana cewa Najeriya, Najeriya a matsayinta na kasa mai tasowa, da wuya ta cika ka’idar .

https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4an-bindiga-ke-lalata-ta-matan-mutane/

Majalisar Duniya da kuma kimar Hukumar Lafiya ta Duniya na samar da likita daya ga marasa lafiya 600.A bangare guda kuma, ministan ya dage kan cewa Najeriya na da isassun likitocin da za su kula da mutane, yana mai cewa matsalar likitocin ita ce ba a turawa da rarraba ma’aikatan kiwon lafiya daidai gwargwado a wuraren da suka dace.

Ya ce yawancin likitocin kasar nan basu son aiki a yankunan karkara, sun zabi yin aikinsu a birane irinsu Abuja, Legas da Fatakwal.

Baya ga kwararrun likitocin cikin gida, Ngige ya ce likitocin da aka horar daga kasashen waje suma suna dawowa Najeriya don yin aiki.Rahoto: Jerin manyan jihohi 10 da suka fi yawan kwararrun likitoci a NajeriyaLikitocin Najeriya | Hoto: guardian.ng Asali: UGC

https://apahausa.com.ng/video-kai-jamaa-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-koma-tamkar-indiyawa/

Ministan ya yi ikirarin cewa a yanzu Najeriya tana da likitoci “kusan 4000 da ‘yan kai”, inda ya dage cewa rashin kwararrun likitoci na da nasaba da rashin daidaita aikin.

Yace: “Don haka, kusan kowa ya tafi Abuja, Legas da Fatakwal don zama. Kuma muna da cibiyoyin kula da lafiya na farko 10,000 wadanda aka yi watsu da su kamar yadda aka yi a kidaya ta karshe.”

Bayanan da Legit.ng ta samu, sun samo asali ne daga Majalisar Likitocin Hakori ta Najeriya.Manyan jihohi 10 mafiya yawan manyan likitoci (alkaluman 2019)Lagos – 2561FCT – 2523Ribas – 917Oyo – 772Edo – 727Kaduna – 711Kano – 632Delta – 554Anambra – 552Filato – 538Sauran jihohin NajeriyaOsun – 536Enugu – 491Ogun – 478Kwara – 446Borno – 377Bayelsa – 359Benue – 332Cross Riba – 330Imo – 319Ondo – 293Abiya – 289Gombe – 286Akwa Ibom – 278Katsina – 266Ekiti – 261Nasarawa – 258Bauchi – 243Kogi – 218Neja – 217Sokoto – 201Ebonyi – 184Adamawa – 147Kebbi – 144Zamfara – 137Yobe – 133Jigawa – 131Taraba – 86Rahoton ya ci gaba da nuna cewa, tun daga shekarar 2019, Najeriya tana da likitoci 6,713 da ba a tantance su a karkashin kowace jiha ba. Adadin likitocin a kasar ya kai 24,640.Sai dai, wani rahoto na baya-bayan nan da aka baiwa Hukumar Kula da Lafiya ta Najeriya ya bayyana cewa kusan likitoci 35,000 ne ke aikin a Najeriya.Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa, likitocin da ke aiki 35,000 suna cikin jimillar likitoci 80,000 da suka yi rajista da Hukumar Kula da Likitoci ta Najeriya (MDCN).

Wasu da ba sa aiki a Najeriya ana kyautata zaton cewa suna aiki a kasashen waje yayin da kadan daga ciki suka sauya sana’o’i.

Views: 40

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *