Ku kalli abinda Fantami ya ce game da sahihancin Pi-Network

Pi-Network wani nau’i ne daga cikin nau’ikan silallan da ba’a ganinsu waɗanda ake gudanar da cinikayyar hada hada dasu a shafukan yanar gizo na Internet.

Wannan kuɗi na Pi ana hasashen cewa zai fi ko wane kuɗi tsada da kuma daraja idan aka ƙaddamar da shi ya zagaya duniya.

To sai dai akwai maganganu sosai game wannan sabon tsari na Pinetwork, wanda har takai ana danganta shi manyan mutane mashahuran malamai da sarakuna.

Wani rahoto da sashin hausa na APA ya ci karo dashi na cewa hatta ministan sadarwa na ƙasa Dr. Isa Ali Fantami ya yi magana game da sahihancin wannan kuɗi na Pi sai dai muna ci gaba da bibiyar sahihancin wannan labarin.

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *