Ku kalli matashin da ya ce ba zai kara yin Sallah ba saboda an yi masa Askin dole

Matashin Da Yace Ya Bar Sallah

A karshen makon daya gabata ne dai wannan matashin ya bayyana cewa shi kam ya daina yin Sallah saboda jami’an hukumar Hisbah sun yi masa aski ta karfi da yaji, wani hoton bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta na zamani ne ya nuna matashin na cewa.

“Wallahi tallahi ba zan kara yin Sallah ba na barta kenan idan na kara yin Sallah Allah ya tsine min albarka” kamar yadda aka nuno shi yana fada a cikin fai fan bidiyon, sai dai daga bisani an nuno shi a wani faifan bidiyon yana yin Alwala zai yi Sallar bayan an yi masa nasiha.

Lokacin Da Yake Yin Alwala Bayan Ya Tuba

Sai dai a wani labarin ya ambato hukumar Hizbah ta jihar Kano ta karyata maganar yiwa wannan matashi aski,

Hukumar tace batayiwa Wannan matashi aski da Bulala Talatin ba, Kuma ko acikin bidiyon da yake yawo A Kafar Sadarwa Basuji In da Matashin yace Hukumar ce Tai Masa Askin ba duk da itama hukumar ta kanyiwa Mutane Aski

Kamar yadda Shugaban Hukumar Hizba Na Jahar Kano Sheikh Haroun Ibni Sina ya Bayyana.

Shin Mezakuce?

Views: 46

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *