
A shekarar 2019 data gabata ne wasu mabambantan hotunan bidiyo suka rika yawo a kusan illahirin kafafen sada zumunta na zamani wato Social Media, inda aka rika nuno magidanta suna zaune matansu na yi musu rawa da rangwada.
A wancen lokacin wakar da aka rika amfani da ita ita ce “Jarumar Mata” wacce shahararren mawakin hausar nan Hamisu Breaker ya rera.
Sai kuma gashi a hakin yanzu ma irin wadannan bidiyoyi sun soma kunno kai inda ma’auratan ke amfani da wakar “Nashiga So” ta MG Boy yanzu haka dai zaku iya kallon bidiyon wakokin a shafukan sada zumunta na YouTube, TikTok da dai sauransu.
Views: 371
