
Wata majiya mai karfi daga jihar Zamfara na cewa, sojojin Najeriya sun shafe yini da daren jiya suna ta luguden wuta ta sama da ta kasa a kan sansanin yan bindigar Zamfara inda Rahotanni ke nuna cewa sojojin su kone illahirin dajin baki daya.
Idan ba’a manta ba a farkon makonnan ne gwamnatin Najeriya ta toshe illahirin hanyoyin sadarwa a jihar ta Zamfara, da zummar kawo karshen yan bindigar da suka addabi yankin arewacin Najeriya gaba daya.
Rahotanni dai sun bayyana cewa a halin yanzu babu abinda ya rage cikin dajin sai dai ana kyautata zaton wata kila son gira ramuka sun boye kansu a cikin, wanda a halin yanzu ana ci gaba da bi lungu da sako na dajin domin zakulo su.
Muna fatan Allah ya kara basu nasara a kan wadannan yan ta’adda ameen.
Views: 96
