LABARI DA DUMI DUMI: Ummi Rahab ta tonawa Adam A Zango asiri

Wasu na ganin wanan magana da jarumar tayi ita kadai ta isa ta bayyana cewa wani abu maras kyau ne ya raba ta da Adam a zango kuma tamkar tonon silili ne ga jarumi, inda ta ce “Naji Kana Faɗa Cewa Wai Kana So Ka Bani Tarbiyya Amma Na Bijire Maka. Idan Ka Cigaba Da Neman Ɓata Min Suna Da Wannan Sharrin Wallahi Zan Tona Ma Asiri”

–Gargaɗin Jaruma Ummi Rahab Ga Tsohon Ubangidanta, Adam A. Zango, Tare Da Ƙarin, “In Kunne Ya Ji.

idan baku manta ba jarumin Adam A Zango ya sallami jaruma umme Rahab daga shirinsa na Farin Wata Sha Kallo wanda har yanzu baa san dalilinsa na yin hakan ba daga bisani ma har ya maye gurbinta.

Sai dai mutane da dama suna ta sake sake da kai kawo a cikin zuciyoyinsu don gano dalilin jarumin na daukar wanna mataki wanda hakan yaci tura gabanin ta fitar da wanna sako daga nata bangare.

Views: 34

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *